Psalms 9
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda. 1Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
2Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikinka;
zan rera yabo ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka.
3Abokan gābana sun ja da baya;
suka yi tuntuɓe suka hallaka a gabanka.
4Gama ka tabbata da gaskiyata da kuma abin da nake yi;
ka zauna a kujerarka, kana yin shari’a da adalci.
5Ka tsawata wa ƙasashe ka kuma hallakar da mugaye;
ka shafe sunansu har abada abadin.
6Lalaci marar ƙarewa ya cimma abokan gābanmu,
ka tuttumɓuke biranensu;
yadda ma ba aka ƙara tunaninsu.
7 Ubangiji yana mulki har abada;
ya kafa kujerarsa don shari’a.
8Zai hukunta duniya da adalci;
zai yi mulkin mutane cikin gaskiya.
9 Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya,
mafaka a lokutan wahala.
10Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
11Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona;
yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.
12Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna;
ba ya ƙyale kukan masu wahala.
13Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini!
Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
14don in furta yabanka
cikin ƙofofin’Yar Sihiyona
a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.
15Al’umma sun fāɗa cikin ramin da suka haƙa wa waɗansu;
aka kama ƙafafunsu a ragar da suka ɓoye.
16An san Ubangiji ta wurin gaskiyarsa;
an kama mugaye da aikin hannuwansu. Haggayiyon. ▼
▼Ko kuwa Tunani; mai yiwuwa salon kiɗi ne.
Sela17Mugaye za su koma kabari,
dukan al’umman da suka manta da Allah.
18Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba,
ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.
19Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara;
bari a hukunta al’ummai a gabanka.
20Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji;
bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela
Copyright information for
HauSRK