‏ Psalms 90

LITTAFI NA HUƊU

Zabura 90–106

Addu’ar Musa Mutumin Allah.

1Ubangiji kai ne mazauninmu
cikin dukan zamanai.
2Kafin a haifi duwatsu
ko a fid da ƙasa da duniya,
daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.

3Ka komar da mutane zuwa ƙura,
kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku’ya’yan mutane.”
4Gama shekaru dubu a gabanka
kamar kwana ɗaya ne da ya wuce,
ko sa’a guda na dare.
5Ka share mutane cikin barcin mutuwa;
suna kama da sabuwa ciyawar safiya,
6ko da yake da safe takan yi sabuwar huda
da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane.

7An cinye mu ta wurin fushinka
mun kuma razana ta wurin hasalarka.
8Ka ajiye laifinmu a gabanka,
asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.
9Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka;
mun gama shekarunmu da nishi.
10Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne,
ko tamanin, in muna da ƙarfi;
duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai,
gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare.
11Wa ya san ƙarfin fushinka?
Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai.
12Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai,
don mu sami zuciyar hikima.

13Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba?
Ka ji tausayin bayinka.
14Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa,
don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu.
15Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba,
kamar yawan shekarun da muka ga wahala.
16Bari a nuna ayyukanka ga bayinka,
darajarka ga’ya’yansu.

17Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu;
ka albarkaci mana aikin hannuwanmu,
I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.
Copyright information for HauSRK