Psalms 91
1Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukakazai huta a cikin inuwar Maɗaukaki. ▼
▼Da Ibraniyanci Shaddai
2Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara.”
3Tabbatacce zai cece ka
daga tarkon mai farauta
da kuma daga cututtuka masu kisa.
4Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
7Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
8Za ka dai gan da idanunka
yadda ake hukunta mugaye.
9In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,
har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
10to, babu wani mugun abin da zai same ka,
ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
11Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai
don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
12za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
13Za ka taka zaki da gamsheƙa;
za ka tattake babban zaki da maciji.
14 Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi;
zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.
15Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa;
zan kasance tare da shi a lokacin wahala,
zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
16Da tsawon rai zan ƙosar da shi
in kuma nuna masa cetona.”
Copyright information for
HauSRK