‏ Psalms 92

Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci.

1Yana da kyau a yabi Ubangiji
a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,
2don a yi shelar ƙaunarka da safe
amincinka kuma da dare,
3da kiɗin molo mai tsirkiya goma
da kuma ƙarar garaya.

4Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji;
na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.
5Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji,
tunaninka da zurfi suke ƙwarai!
6Mutum marar azanci ba zai sani ba,
wawa ba zai gane ba,
7cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa
kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka,
za a hallaka su har abada.

8Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.

9Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji,
tabbatacce abokan gābanka za su hallaka;
za a watsar da dukan masu aikata mugunta.
10Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna;
an zubo mai masu kyau a kaina.
11Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana;
kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.

12Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino,
za su yi girma kama al’ul na Lebanon;
13da aka daddasa a gidan Ubangiji,
za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.
14Za su ci gaba da ba da’ya’ya a tsufansu,
za su kasance ɗanye kuma kore shar,
15suna shela cewa, “Ubangiji adali ne;
shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”
Copyright information for HauSRK