Psalms 93
1Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka;Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi.
An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.
2An kafa kursiyin tun da daɗewa;
kana nan tun fil azal.
3Tekuna sun taso, ya Ubangiji,
tekuna sun ta da muryarsu;
tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.
4Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye,
mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku,
Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.
5Ƙa’idodinka suna nan daram;
tsarki ya yi wa gidanka ado
har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK