‏ Psalms 94

1Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa,
Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.
2Ka tashi, ya Alƙalin duniya;
ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.
3Har yaushe mugaye, ya Ubangiji
har yaushe mugaye za su yi ta murna?

4Suna ta yin maganganun fariya;
dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.
5Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji;
suna danne gādonka.
6Suna kashe gwauraye da kuma baƙi;
suna kisan marayu.
7Suna ce, “Ubangiji ba ya gani;
Allah na Yaƙub bai kula ba.”

8Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane;
ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?
9Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne?
Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?
10Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne?
Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
11 Ubangiji ya san tunanin mutum;
ya san cewa tunaninsu banza ne.

12Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji,
mutumin da ka koyar daga dokarka;
13kana ba shi sauƙi a lokacin wahala,
sai har an haƙa rami wa mugaye.
14Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba;
ba zai taɓa yashe gādonsa ba.
15Za a sāke kafa hukunci a kan adalci,
kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.

16Wane ne zai yi gāba da mugaye domina?
Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?
17Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba,
da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.
18Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,”
ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.
19Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina,
ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.

20Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai,
wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?
21Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci
suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.
22Amma Ubangiji ya zama kagarata,
Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.
23Zai sāka musu saboda zunubansu
yă kuma hallaka su saboda muguntarsu;
Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.
Copyright information for HauSRK