‏ Psalms 95

1Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji;
bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.
2Bari mu zo gabansa da godiya
mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.

3Gama Ubangiji Allah mai girma ne,
babban Sarki a bisa dukan alloli.
4A hannunsa ne zurfafan duniya suke,
ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.
5Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi,
da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.

6Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,
bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
7gama shi ne Allahnmu
mu mutanen makiyayansa ne,
garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa.

Yau, in kuka ji muryarsa,
8“Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba,
Meriba yana nufin faɗa.

kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa
Massa yana nufin gwaji.
a hamada,
9inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni,
ko da yake sun ga abin da na yi.
10Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara;
na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce,
kuma ba su san hanyoyina ba.’
11Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina,
‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”
Copyright information for HauSRK