‏ Psalms 97

1Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna;
bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki.
2Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi;
adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.
3Wuta tana tafiya a gabansa
tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe.
4Walƙiyarsa ta haskaka duniya;
duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki.
5Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji,
a gaban Ubangijin dukan duniya.
6Sammai sun yi shelar adalcinsa,
dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.

7Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya,
waɗanda suke fariya da gumaka,
ku yi masa sujada, dukanku alloli!

8Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki
kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna
saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.
9Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya;
ana darjanta ka fiye da dukan alloli.
10Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta,
gama yana tsaron rayukan amintattunsa
yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
11An haskaka haske a kan masu adalci
da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.
12Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci,
ku kuma yabi sunansa mai tsarki.
Copyright information for HauSRK