Psalms 98
Zabura ce. 1Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,gama ya yi abubuwa masu banmamaki;
hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki
sun yi masa aikin ceto.
2 Ubangiji ya sanar da cetonsa
ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.
3Ya tuna da ƙaunarsa
da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila;
dukan iyakar duniya sun ga
ceton Allahnmu.
4Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya,
ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
5ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya,
da garaya da ƙarar rerawa,
6tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago,
ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
7Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa,
duniya da kuma kome da yake cikinta.
8Bari koguna su tafa hannuwansu,
bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
9bari su rera a gaban Ubangiji,
gama yana zuwa domin yă hukunta duniya.
Zai hukunta duniya da adalci
mutane kuma cikin gaskiya.
Copyright information for
HauSRK