Song of Solomon 3
1Dare farai a kan gadonana nemi wanda zuciyata take ƙauna;
na neme shi amma ban same shi ba.
2Zan tashi yanzu in zagaya gari,
in ratsa titunansa da dandalinsa;
zan nemi wanda zuciyata take ƙauna.
Saboda haka na neme shi, amma ban same shi ba.
3Masu tsaro suka gamu da ni
yayinda suke kai kawo a cikin birni, sai na ce,
“Kun ga mini wanda zuciyata take ƙauna?”
4Rabuwata da su ke nan
sai na sami wanda zuciyata take ƙauna.
Na riƙe shi, ban yarda yă tafi ba
sai da na kawo shi gidan mahaifiyata,
zuwa ɗakin wadda ta yi cikina.
5’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari
da bareyi da ƙishimai na jeji.
Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba
sai haka ya zama lalle.
6Wane ne wannan mai zuwa daga hamada
kamar tunnuƙewar hayaƙi,
cike da ƙanshin turaren mur da lubban
da aka yi da kayan yajin’yan kasuwa?
7Duba! Abin ɗaukar Solomon ne,
jarumawa sittin suke rakiya,
zaɓaɓɓun sojojin Isra’ila,
8dukansu suna saye da takobi
dukansu ƙwararru ne a yaƙi,
kowanne da takobinsa a rataye a gefensa,
a shirye don abubuwan bantsoro na dare.
9Sarki Solomon ya yi wa kansa abin ɗauka;
ya yi shi da katako daga Lebanon.
10An yi sandunansa da azurfa,
aka yi ƙasarsa da zinariya.
An lulluɓe wurin zaman da zanen shunayya,
’yan matan Urushalima sun yi mata irin yayen da ake yi na ƙauna.
11Fito, ku’yan matan Sihiyona,
ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani,
rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa,
a ranar aurensa,
a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.
Copyright information for
HauSRK