Song of Solomon 7
1Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne,Ya diyar sarki!
Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja,
aikin hannun gwanin sassaƙa.
2Cibinki kamar kwaf ne
da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba.
Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama
wanda furen bi-rana ya kewaye.
3Nonanki sun yi kamar bareyi biyu,
tagwayen barewa.
4Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa.
Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon
kusa da ƙofar Bat Rabbim.
Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon
wadda take duban Damaskus.
5Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel.
Gashinki ya yi kamar shunayya;
yakan ɗauke hankalin sarki.
6Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi,
Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo!
7Tsayinki ya yi kamar itacen dabino,
kuma nonanki sun yi kamar’ya’yan itace.
8Na ce, “Zan hau itacen dabino;
zan kama’ya’yansa.”
Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa,
ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa,
9kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau.
Ƙaunatacciya Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena,
yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora.
10Ni ta ƙaunataccena ce,
kuma sha’awarsa domina ne.
11Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari,
bari mu kwana a ƙauye.
12Bari mu tafi gonar inabi da sassafe
don mu ga ko kuringar ta yi’ya’ya,
ko furanninsu sun buɗe,
ko rumman sun yi fure,
a can zan nuna maka ƙaunata.
13Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu,
a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi,
sabo da tsoho,
da na ajiye dominka, ƙaunataccena.
Copyright information for
HauSRK