‏ Zechariah 10

Ubangiji zai lura da Yahuda

1Ku roƙi Ubangiji yă ba ku ruwa a lokacin bazara;
Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari.
Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama
yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.
2Gumaka suna maganganun ruɗu,
masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya,
suna faɗa mafarkan ƙarya
suna ba da ta’aziyyar banza.
Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki
waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.

3“Ina fushi da makiyayan,
zan kuma hukunta shugabannin;
gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura
da garkensa, wato, gidan Yahuda,
zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.
4Daga Yahuda dutsen kusurwa zai fito,
daga gare shi za a samu abin kafa tenti,
daga gare shi za a sami bakan yaƙi,
daga gare shi za a sami kowane mai mulki.
5Tare za su
Ko kuwa mai mulki, dukansu tare. 5 Su
zama kamar mutane masu ƙarfi
suna tattake lakar tituna a cikin yaƙi.
Domin Ubangiji yana tare da su,
za su yi faɗa su kuma yi nasara a kan masu yaƙi a kan dawakai.

6“Zan ƙarfafa gidan Yahuda
in kuma ceci gidan Yusuf.
Zan maido da su
domin ina jin tausayinsu.
Za su zama kamar
ban taɓa ƙinsu ba,
gama ni ne Ubangiji Allahnsu
zan kuma amsa musu.
7Mutanen Efraim za su zama kamar mutane masu ƙarfi,
zukatansu kuwa za su yi murna kamar sun sha ruwan inabi.
’Ya’yansu za su gani su yi murna;
zuciyarsu za tă yi farin ciki a cikin Ubangiji.
8Zan ba da alama
in kuma tattara su.
Ba shakka zan fanshe su;
za su yi yawa kamar yadda suke a dā.
9Ko da yake na warwatsa su cikin mutane,
duk da haka a can ƙasashe masu nisa za su tuna da ni.
Su da’ya’yansu za su rayu,
za su kuwa komo.
10Zan komo da su daga Masar
in kuma tattara su daga Assuriya.
Zan kawo su Gileyad da Lebanon,
har wuri yă kāsa musu.
11Za su ratsa cikin tekun wahala;
zan kwantar da raƙuman teku
dukan zurfafan Nilu kuma za su bushe.
Za a ƙasƙantar da Assuriya,
sandar sarautar Masar kuma za tă rabu da ita.
12Zan ƙarfafa su a cikin Ubangiji
kuma a cikin sunansa za su yi tafiya,”
in ji Ubangiji.
Copyright information for HauSRK