Zechariah 9
Hukunci a kan abokan gāban Isra’ila
1Annabci. Maganar Ubangiji tana gāba da ƙasar Hadrakza tă kuma sauko a kan Damaskus,
gama idanun dukan mutane da na kabilan Isra’ila
suna a kan Ubangiji ▼
▼Ko kuwa Damaskus. Gama idon Ubangiji yana a kan dukan mutane, haka ma a kan kabilan Isra’ila,
,2da kuma a kan Hamat ita ma, wadda ta yi iyaka da ita,
da kuma a kan Taya da Sidon, ko da yake suna da hikima ƙwarai.
3Taya ta gina wa kanta mafaka mai ƙarfi;
ta tara azurfa kamar ƙasa,
zinariya kuma kamar tarin shara a tituna.
4Amma Ubangiji zai karɓe mallakarta,
zai hallaka ikonta da take da shi a kan teku,
wuta kuma za tă cinye ta.
5Ashkelon za tă ga haka ta ji tsoro;
Gaza za tă yi birgima cikin azaba,
haka Ekron ma, gama za tă fid da zuciya.
Gaza za tă rasa sarkinta
za a kuma gudu a bar Ashkelon.
6Baƙi za su mallaki Ashdod,
kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.
7Zan kawar da jini daga bakinsu,
zan kuma cire abincin da aka haramta daga tsakanin haƙoransu.
Waɗanda za a bari za su zama na Allahnmu,
su kuma zama shugabanni a Yahuda,
Ekron kuma za tă zama kamar Yebusiyawa.
8Amma zan kāre gidana
daga sojoji masu kai da kawowa.
Azzalumi ba zai ƙara cin mutanena da yaƙi ba,
gama yanzu ina tsaro.
Zuwan sarkin Sihiyona
9Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima!Ki yi sowa, Diyar Urushalima!
Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki,
mai adalci yana kuma da ceto,
mai tawali’u yana kuma hawan jaki,
yana a kan ɗan aholaki, a kan’yar jaka.
10Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim,
da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima,
za a kuma karya bakan yaƙi.
Zai yi shelar salama ga al’ummai.
Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku,
daga Kogi ▼
▼Wato, Yuferites
kuma zuwa ƙarshen duniya. ▼▼Ko kuwa ƙarshen ƙasa
11Ke kuma, saboda jinin alkawarina da ke,
zan’yantar da’yan kurkukunki daga rami marar ruwa.
12Ku koma maɓuya, ya ku’yan kurkuku masu sa zuciya;
ko yanzu ma na sanar cewa zan mayar muku ninki biyu.
13Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana,
in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya.
Zan tā da’ya’yanki maza, ya Sihiyona,
gāba da’ya’yanki, ya Girka,
in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.
Ubangiji zai bayyana
14Sa’an nan Ubangiji zai bayyana a bisansu;kibiyarsa za tă wulga kamar walƙiya.
Ubangiji Mai Iko Duka zai busa ƙaho;
zai taho ta cikin guguwa daga kudu,
15 Ubangiji Maɗaukaki kuma zai tsare su.
Za su hallakar
su kuma yi nasara da duwatsun majajjawa.
Za su sha su yi kururuwa kamar sun sha ruwan inabi;
za su cika kamar kwanon
da ake amfani don a yayyafa jini a kusurwoyin bagade.
16 Ubangiji Allahnsu zai cece su a wannan rana
gama su mutanensa ne da kuma garkensa.
Za su haska a cikin ƙasarsa
kamar lu’ulu’u a rawani.
17Za su yi kyan gani da kuma bansha’awa!
Hatsi zai sa samari su yi murna,
sabon ruwan inabi kuma zai sa’yan mata su yi farin ciki.
Copyright information for
HauSRK