‏ 1 Chronicles 11:20-47

(2 Sama’ila 23.18-39)

20Abishai ɗan’uwan Yowab shi ma babba ne cikin Ukun nan. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe, ya kuma zama sananne kamar Ukun. 21Aka ninka girmama shi bisa Ukun, sai ya zama shugaba, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.

22Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki. 23Ya kuma kashe wani mutumin Masar mai tsayi ƙafa bakwai da rabi. Ko da yake mutumin Masar yana da māshi kamar sandan masaƙa a hannunsa, Benahiya ya yaƙe shi da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannun mutumin Masar ya kuma kashe shi da māshin nan nasa. 24Irin abubuwan da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma sananne ne kamar waɗannan jarumawa uku. 25Aka ɗauka shi da bangirma fiye da Talatin nan, amma ba a haɗa shi cikin Ukun ba. Dawuda kuwa ya sa shi yă lura da masu tsaron lafiyarsa.

26Jarumawan nan su ne,

Asahel ɗan’uwan Yowab,
Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,
27Shammot mutumin Haror,
Helez mutumin Felon,
28Ira ɗan Ikkesh daga Tekowa,
Abiyezer daga Anatot,
29Sibbekai mutumin Husha,
Ilai mutumin Aho,
30Maharai mutumin Netofa,
Heled ɗan Ba’ana mutumin Netofa,
31Ittai ɗan Ribai daga Gibeya a Benyamin,
Benahiya mutumin Firaton,
32Hurai daga kogunan Ga’ash,
Abiyel mutumin Arba,
33Azmawet mutumin Harum,
Eliyaba mutumin Sha’albo,
34’ya’yan Hashem mutumin Gizon maza,
Yonatan ɗan Shageye mutumin Harar,
35Ahiyam ɗan Sakar mutumin Harar,
Elifal ɗan Ur,
36Hefer mutumin Mekerat,
Ahiya mutumin Felon,
37Hezro mutumin Karmel,
Na’arai ɗan Ezbai,
38Yowel ɗan’uwan Natan,
Mibhar ɗan Hagiri,
39Zelek mutumin Ammon
Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya,
40Ira mutumin Itra,
Gareb mutumin Itra,
41Uriya mutumin Hitti
Zabad ɗan Alai,
42Adina ɗan Shiza mutumin Ruben, wanda shi ne babba na mutanen Ruben, kuma talatin suna tare da shi,
43Hanan ɗan Ma’aka,
Yoshafat mutumin Mit,
44Uzziya mutumin Ashtarot,
Shama da Yehiyel’ya’yan Hotam mutumin Arower maza,
45Yediyayel ɗan Shimri,
ɗan’uwansa Yoha mutumin Tiz,
46Eliyel mutumin Ma’aha,
Yeribai da Yoshawiya’ya’yan Elna’am maza,
Itma mutumin Mowab,
47Eliyel, Obed da Ya’asiyel mutumin Mezob.
Copyright information for HauSRK