1 Chronicles 17:16-27
Addu’ar Dawuda
(2 Sama’ila 7.18-29)
16Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan? 17Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah. 18“Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka, 19Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura. 20“Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu. 21Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar? 22Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu. 23“Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari, 24saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka. 25“Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka. 26Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka. 27Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.”
Copyright information for
HauSRK