1 Chronicles 18:14-17
Manyan ma’aikatan Dawuda
(2 Sama’ila 8.15-18)
14Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa. 15Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa;Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;
16Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci;
Shafsha shi ne magatakarda;
17Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa;
’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.
Copyright information for
HauSRK