‏ 1 Chronicles 21:1-6

Dawuda ya ƙidaya mayaƙansa

(2 Sama’ila 24.1-9)

1Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila. 2Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.”

3Amma Yowab ya amsa ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya mayaƙansa fiye da sau ɗari. Ranka yă daɗe sarki, dukansu ba bayin shugabana ba ne? Me ya sa ranka yă daɗe yake so yă yi haka? Me zai sa ka kawo laifi a kan Isra’ila?”

4Amma sarki ya nace a kan maganar da ya yi wa Yowab. Sai Yowab ya tashi ya tafi cikin dukan Isra’ila, ya kewaye sa’an nan ya dawo Urushalima. 5Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.

6Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.
Copyright information for HauSRK