1 Chronicles 8:29-38
29Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon.Sunan matarsa Ma’aka, 30ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab, 31Gedor, Ahiyo, Zeker 32da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
33Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
34Ɗan Yonatan shi ne,
Merib-Ba’al ▼
▼Aka kuma sani kamar Mefiboshet
wanda ya zama mahaifin Mika.35’Ya’yan Mika maza su ne,
Fiton, Melek, Tereya da Ahaz.
36Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. 37Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel.
38Azel yana da’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu.
Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan’ya’yan Azel maza ne.
Copyright information for
HauSRK