1 Kings 10:26-29
26Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai; ya kasance da kekunan yaƙi dubu goma sha huɗu, da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, ya kuma ajiye tare da shi a Urushalima. 27Sarki ya mai da azurfa barkatai a cikin Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir na jumaiza a gindin tuddai. 28An yi jigilar dawakan Solomon daga Masar ▼▼Mai yiwuwa Muzur, wani yanki a Silisiya; haka ma a aya 29.
da kuma daga Kuye ▼▼Mai yiwuwa Silisiya
,’yan kasuwan fadan sarki sun sayo su daga Kuye. 29Suka yi jigilar kekunan yaƙi daga Masar a bakin shekel ɗari shida na azurfa, doki ɗaya kuma a kan ɗari da hamsin. Sun kuma yi jigilarsu suna sayarwa ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa.
Copyright information for
HauSRK