‏ 1 Kings 14:29-31

29Game da sauran ayyukan mulkin Rehobowam kuwa, da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 30Aka ci gaba da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam. 31Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci da Seftuwajin (duba kuma 2Tar 12.16); yawancin rubuce-rubucen hannu na Ibraniyanci suna da Abiya
ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Copyright information for HauSRK