‏ 1 Kings 3:1-15

Solomon ya nemi hikima

(2 Tarihi 1.1-13)

1Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima. 2A lokacin dai mutane suna miƙa hadaya a wurare a bisa tuddai, domin ba a riga an gina haikali saboda Sunan Ubangiji ba. 3Solomon ya ƙaunaci Ubangiji ta wurin yin tafiya bisa ga farillan mahaifinsa Dawuda, sai dai ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a wuraren nan na bisa tuddai.

4Sai sarki Solomon ya tafi Gibeyon don yă miƙa hadayu, gama a can ne wuri mafi muhimmanci na sujada. Solomon kuwa ya miƙa hadayun ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade. 5A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”

6Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana.

7“Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. 8Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. 9Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”

10Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. 11Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, 12zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. 13Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. 14In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.” 15Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne.

Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki.
Copyright information for HauSRK