1 Kings 9:1-9
Ubangiji ya bayyana ga Solomon
(2 Tarihi 7.11-22)
1Sa’ad da Solomon ya gama ginin haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki, ya kuma yi dukan abin da yake so yă yi, 2sai Ubangiji ya bayyana gare shi sau na biyu, kamar yadda ya bayyana masa a Gibeyon. 3Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can. 4“Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina, 5zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’ 6“Amma in kai, ko’ya’yanka maza, suka juye daga gare ni, ba ku kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da na ba ku ba, kuka yi gaba, kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka kuma yi musu sujada, 7sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane. 8Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’ 9Mutane za su amsa su ce, ‘Saboda sun yashe Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna yin musu sujada, suna bauta musu ne, ya sa Ubangiji ya kawo dukan masifan nan a kansu.’ ”
Copyright information for
HauSRK