1 Kings 9:10-28
Waɗansu ayyukan Solomon
(2 Tarihi 8.1-18)
10A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki, 11sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki. 12Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba. 13Sai ya ce, “Wanda irin garuruwa ke nan ka ba ni, ɗan’uwana?” Saboda haka ya kira su Ƙasar Kabul ▼▼Kabul ya yi kamar kalmar Ibraniyanci na abu marar amfani.
, sunan da suke da shi har wa yau. 14Hiram kuwa ya aika wa sarki talenti 120 ▼▼Wato, kamar ton 4 da 1/2 ke nan
na zinariya. 15Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer. 16(Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga’yarsa, matar Solomon. 17Solomon kuwa ya sāke gina Gezer.) Ya gina Bet-Horon ta Kwari, 18da Ba’alat, da Tadmor a hamada, na cikin ƙasarsa. 19Haka kuma ya gina dukan biranen ajiyarsa, da garuruwa domin kekunan yaƙinsa, da garuruwa domin dawakansa. Ya gina duk abin da ya so yă ginawa a Urushalima, da Lebanon, da kuma ko’ina a dukan yankin da ya yi mulki. 20Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa da Yebusiyawan da suka ragu a ƙasar (waɗanda ba Isra’ilawa ba ne), 21wato, waɗanda suka ragu a ƙasar, waɗanda Isra’ilawa ba su iya hallakawa ba, su ne Solomon ya ɗauka su zama bayinsa don aikin gandu, kamar yadda yake har wa yau. 22Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi ba; su ne mayaƙansa, shugabannin gwamnatinsa, dogarawansa, shugabannin sojojinsa, da shugabanninsa na kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙinsa. 23Su ne kuma manyan shugabanni masu lura da ayyukan Solomon, su ne shugabanni 550 masu lura da mutanen da suke aiki. 24Bayan’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini. 25Sau uku a shekara Solomon kan miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji, yana ƙone turare a gaban Ubangiji haɗe da su, ta haka ya cika abin da ake bukata na haikali. 26Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku. 27Hiram kuwa ya aiki mutanensa, masu tuƙan jirgin ruwa waɗanda suka san teku, don su yi hidima a jerin jiragen ruwa tare da mutanen Solomon. 28Suka tafi Ofir suka kuma dawo da talenti 420 na zinariya, wanda suka ba wa Sarki Solomon.
Copyright information for
HauSRK