‏ 2 Chronicles 18:28-34

An kashe Ahab a Ramot Gileyad

(1 Sarakuna 22.29-35)

28Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad. 29Sarkin Isra’ila ya ce wa Yehoshafat, “Zan ɓad da kama in shiga yaƙin, amma ka sa kayanka na sarauta.” Saboda haka sarkin Isra’ila ya ɓad da kama ya shiga cikin yaƙin.

30To, fa, sarkin Aram ya umarce shugabannin keken yaƙinsa ya ce, “Kada ku yaƙi kowa, ƙarami ko babba, sai dai sarkin Isra’ila.” 31Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙi suka ga Yehoshafat, sai suka yi tsammani, “Wannan ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juya don su yaƙe shi, amma Yehoshafat ya yi ihu, Ubangiji kuma ya taimake shi. Allah ya janye su daga gare shi, 32gama sa’ad da shugabannin keken yaƙi suka ga cewa ba shi ne sarkin Isra’ila ba, sai suka daina binsa.

33Amma wani ya harba kibiya haka kawai, sai kibiyar ta sami sarki Ahab na Isra’ila a kafaɗa tsakanin rigar yaƙinsa na ƙarfe da ƙarfen ƙirjinsa. Sai sarki ya ce wa mai tuƙan keken yaƙi, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin. An ji mini rauni.” 34Duk yini yaƙi ya yi ta cin gaba, sarkin Isra’ila kuwa ya jingina kansa a cikin keken yaƙinsa yana duban Arameyawa har yamma. Sa’an nan a fāɗuwar rana sai ya mutu.
Copyright information for HauSRK