‏ 2 Chronicles 35:1-19

Yosiya ya yi Bikin Ƙetarewa

(2 Sarakuna 23.21-23)

1Yosiya ya yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima, aka kuma yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a ranar goma sha huɗu ga wata na farko. 2Ya zaɓi firistoci su yi aikinsu, sai ya ƙarfafa su su yi aikin da kyau a hidimar haikalin Ubangiji. 3Ya ce wa Lawiyawa waɗanda suke koyar da dukan Isra’ila da kuma waɗanda aka tsarkake wa Ubangiji. “Ku sa akwatin alkawari mai tsarki a cikin haikalin da Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila ya gina. Ba za a riƙa ɗaukansa a kafaɗa ba. Yanzu ku bauta wa Ubangiji Allahnku da kuma mutanensa Isra’ila. 4Ku shirya kanku iyali-iyali a sassanku, bisa ga umarnan da Dawuda sarkin Isra’ila da kuma ɗansa Solomon suka rubuta.

5“Ku tsaya a tsattsarkan wuri, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin’yan’uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa. 6Ku yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku kuma shirya raguna domin’yan’uwanku, kuna yin abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.”

7Yosiya ya tanada wa dukan mutanen da ba firistoci ba ne waɗanda suke a wurin, tumaki da awaki dubu talatin don a yanka saboda hadayun Bikin Ƙetarewa, ya kuma ba su shanu dubu uku. Dukan dabbobin kuwa daga garken sarki ne.

8Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku. 9Haka kuma Konaniya tare da Shemahiya da Netanel, ɗan’uwansa, da Hashabiya, Yehiyel da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, suka tanadar da hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyar da kuma bijimai ɗari biyar domin Lawiyawa.

10Sa’ad da aka shirya kome don Bikin Ƙetarewar, sai Firistoci tare da Lawiyawa suka tsaya wurin tsayawarsu bisa ga umarnin sarki. 11Aka yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, firistoci kuma suka yayyafa jinin da aka ba su, yayinda Lawiyawa suna fiɗan dabbobi. 12Suka keɓe hadayun ƙonawa don su ba da su ga ƙungiyoyin iyalan mutane don su miƙa ga Ubangiji, yadda yake a rubuce a Littafin Musa. Suka yi haka da shanun. 13Suka gasa dabbobin Bikin Ƙetarewa a bisa wuta yadda aka tsara, suka dafa hadayu masu tsarki a tukwane, da manyan tukwane, da kuma kwanoni, suka raba su nan da nan ga dukan mutane. 14Bayan wannan, suka shirya wa kansu da kuma wa firistoci, saboda firistoci, zuriyar Haruna, suna miƙa hadayun ƙonawa da sashen kitse daga safe har dare. Saboda haka Lawiyawa suka shirya wa kansu da kuma wa firistocin daga zuriyar Haruna.

15Mawaƙa zuriyar Asaf, suna a wuraren da Dawuda, Asaf, Heman da Yedutun mai duba na sarki suka tsara. Bai zama lalle matsaran ƙofofi a kowace ƙofa su bar wuraren aikinsu ba, domin’yan’uwansu Lawiyawa sun yi shiri dominsu.

16Ta haka fa aka yi dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Bikin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda sarki Yosiya ya umarta. 17Isra’ilawan da suka kasance a can suka yi Bikin Ƙetarewa a wannan rana, suka kuma kiyaye Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai. 18Ba a taɓa yin Bikin Ƙetarewa haka ba tun zamanin annabi Sama’ila; kuma babu sarkin Isra’ilan da ya taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci, Lawiyawa da kuma dukan Yahuda da Isra’ila, waɗanda suke can tare da mutanen Urushalima. 19An yi wannan Bikin Ƙetarewa a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya.
Copyright information for HauSRK