‏ 2 Chronicles 4:1-10

Kayayyakin haikalin

(1 Sarakuna 7.23-51)

1Ya yi bagaden tagulla mai tsawo kamu ashirin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu goma. 2Ya yi ƙaton kwano mai suna Teku na zubin ƙarfe, mai siffar da’ira, awonsa kamu goma ne daga da’ira zuwa da’ira tsayinsa kuma kamu biyar. Ya ɗauki magwaji mai tsawo kamu talatin ya auna shi kewaye. 3Ƙasa da da’ira kuwa, akwai siffofin bijimai kewaye da ita, goma ga kowane kamu guda. An yi zubin bijiman a jeri biyu a gefe guda na kwatarniya.

4Tekun ya tsaya a kan bijimai goma sha biyu, uku na fuskantar arewa, uku na fuskantar yamma, uku na fuskantar kudu, uku kuma na fuskantar gabas. Tekun ya zauna a kansu, kuma ƙarfafun bayansu suna wajen tsakiya. 5Kaurin ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kama da’irar kwaf, kama furen da ya tohu. Ya riƙe randuna dubu uku.

6Sa’an nan ya yi daruna goma don wanki ya sa biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. A cikinsu kayan da za a yi amfani don ɗauraye hadayun ƙonawa, amma firistoci suna amfani da ƙaton kwano mai suna Teku don wanki.

7Ya yi wurin ajiye fitila goma na zinariya bisa ga tsari dominsu ya kuma sa su a haikali, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa.

8Ya yi tebur goma ya kuma sa su cikin haikalin, biyar a gefen kudu, biyar kuma a gefen arewa. Ya kuma yi kwanonin yayyafawa guda ɗari.

9Ya yi fili na firistoci da kuma babban fili da ƙofofi domin filin, ya shafe ƙofofin da tagulla. 10Ya sa ƙaton kwano mai suna Teku a gefen kudu, a kusurwa kudu maso gabas.
Copyright information for HauSRK