‏ 2 Chronicles 9:13-28

Ɗaukakar Solomon

13Nauyin zinariyar da Solomon yake karɓa shekara-shekara talenti 666 ne, 14ban da harajin da fatakai da’yan kasuwa suke biya. Haka kuma dukan sarakunan Arabiya da gwamnonin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa wa Solomon.

15Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu da zinariya; an yi kowane garkuwa da bekas ɗari shida na zinariya. 16Ya kuma yi ƙanana garkuwoyi zinariya ɗari uku, da bekas ɗari uku na zinariya a kowanne. Sarki ya sa su a cikin Fadan da ake kira Kurmin Lebanon.

17Sai sarki ya yi wata kujerar sarauta mai girma da aka shafe ta da hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla. 18Kujerar tana da matakalai shida, da wurin sa ƙafa na zinariya haɗe da ita. A kowane gefen wurin zama, akwai wurin ajiye hannu, da zaki tsaye kusa da kowannensu. 19Zakoki goma sha biyu sun tsaya a kan matakalai shida, ɗaya a ƙarshen matakala guda. Ba a taɓa yin irin wannan abu don wata masarauta ba. 20Dukan kwaf na Sarki Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon zinariya ne zalla. Ba a yi wani abu da azurfa ba, domin ba a ɗauki azurfa a zamanin Solomon a bakin kome ba. 21Sarki yana da jerin jiragen ruwa na kasuwanci waɗanda mutanen Hiram ne suke kula da su. Sau ɗaya kowace shekara uku sukan dawo ɗauke da zinariya, azurfa, hauren giwa, gogo da kuma birai.

22Sarki Solomon ya fi arziki da hikima in aka kwatanta da dukan sauran sarakunan duniya. 23Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa. 24Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai.

25Solomon ya kasance da wuraren ajiye dawakai dubu huɗu don dawakai da kekunan yaƙi, yana da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi da kuma tare da shi a Urushalima. 26Ya yi mulki bisa dukan sarakuna daga Kogi Yuferites zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. 27Sarki ya sa azurfa ta zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka. 28An sayo dawakan Solomon daga Masar da kuma daga dukan sauran ƙasashe.
Copyright information for HauSRK