‏ 2 Kings 11:1-3

Ataliya da Yowash

(2 Tarihi 22.10-12)

1Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta. 2Amma Yehosheba,’yar Sarki Yoram
Da Ibraniyanci Yehoram, wani suna na Yehoram
,’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.
3Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
Copyright information for HauSRK