2 Kings 14:1-6
Amaziya sarkin Yahuda
(2 Tarihi 25.1-24)
1A shekara ta biyu ta mulkin Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila, Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya fara mulki. 2Ya zama sarki yana da shekaru ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin, mutuniyar Urushalima. 3Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, sai dai ba kamar kakansa Dawuda ba. A kome dai ya bi gurbin mahaifinsa Yowash. 4Ba a dai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙone turare a can. 5Bayan masarauta ta kahu a hannunsa, sai ya kashe fadawan da suka kashe mahaifinsa sarki. 6Duk da haka bai kashe’ya’yan masu kisan ba, bisa ga abin da yake a rubuce a Dokar Musa inda Ubangiji ya umarta, “Ba za a kashe iyaye saboda laifin’ya’ya ba, ko kuma’ya’ya saboda laifin iyayensu ba, kowa zai mutu don zunubansa.” ▼▼M Sh 24.16.
Copyright information for
HauSRK