‏ 2 Kings 19:20-34

Ishaya ya yi annabcin fāɗuwar Sennakerib

(Ishaya 37.21-35)

20Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya. 21Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi, “ ‘Budurwar Sihiyona
ta rena ka tana kuma yin maka ba’a.
Diyar Urushalima
ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.
22Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo?
Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka,
har ka tā da idanunka da fahariya?
Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!
23Ta wurin manzanninka
ka tara wa Ubangiji zagi.
Ka kuma ce,
“Da yawa kekunan yaƙina
na haye kan ƙwanƙolin duwatsu,
wurin mafi tsawo na Lebanon.
Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo
mafi daraja na itacen fir nasa.
Na ratsa har can tsakiyar kurmi,
mafi kyau na kurminsa.
24Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje
na kuma sha ruwa a can.
Da tafin ƙafafuna
na busar da dukan rafuffukan Masar.”

25“ ‘Ba ka taɓa ji ba?
Tun da daɗewa na ƙaddara haka.
Tuntuni kuwa na shirya shi;
yanzu kuma na sa ya faru,
cewa ka mai da birane masu katanga
tarin duwatsu.
26Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye,
suka razana aka kuma kunyata su.
Suna kama da tsirai a gona,
kamar sabon toho
kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki
wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.

27“ ‘Amma na san wurin zamanka
da fitarka da shigarka
da yadda kake fushi da ni.
28Domin kana fushi da ni
reninka ya iso kunnuwata,
zan sa ƙugiyata a hancinka
da linzamina a bakinka,
zan kuma sa ka koma
a ta hanyar da ka zo.’

29“Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya, “Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa,
baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara.
Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe,
ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci’ya’yansa.
30Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda
za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da’ya’ya a bisa.
31Gama daga Urushalima za a sami ragowa,
daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira.

Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.

32“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga birnin nan ba
ko yă harba kibiya a nan.
Ba zai kusace ta da garkuwa
ko yă yi mata zoben yaƙi ba.
33Ta hanyar da ya zo ne zai koma;
ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.
34Zan kāre birnin nan in cece ta,
saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”
Copyright information for HauSRK