‏ 2 Kings 21:19-26

Amon sarkin Yahuda

(2 Tarihi 33.21-25)

19Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce. 20Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi. 21Ya bi duk gurbin mahaifinsa a kome, ya yi sujada ga gumakan da mahaifinsa ya yi wa, ya kuma durƙusa musu. 22Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba.

23Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa. 24Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.

25Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 26Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi.
Copyright information for HauSRK