2 Kings 25:27-30
An saki Yehohiyacin
(Irmiya 52.31-34)
27A shekara ta talatin da bakwai ta bautar Yehohiyacin sarkin Yahuda, a shekaran da Ewil-Merodak ▼▼Da ake kuma kira Amel-Marduk
ya ci sarautan Babilon, sai ya saki Yehohiyacin daga jaru, ya sake shi a rana ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu. 28Ya yi wa Yehohiyacin maganar alheri, ya kuma ɗaukaka shi sama da sauran sarakunan da suke tare da shi a Babilon. 29Don haka Yehohiyacin ya tuɓe kayan fursuna. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har iyakar ransa. 30Sarki kuma ya yanka masa kuɗin da za a dinga ba shi, kowace rana muddin ransa.
Copyright information for
HauSRK