2 Kings 8:16-24
Yehoram sarkin Yahuda
(2 Tarihi 21.2-20)
16A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda. 17Yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki na tsawon shekara takwas a Urushalima. 18Ya bi gurbin sarakunan Isra’ila, yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri’yar Ahab. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji. 19Duk da haka, saboda bawansa Dawuda, Ubangiji bai ragargaza Yahuda ba. Ya riga ya yi alkawari zai bar wa Dawuda magāji har abada. 20A kwanakin Yoram, Edom ta yi wa Yahuda tawaye, ta naɗa wa kanta sarki. 21Saboda haka Yehoram ya tafi Zayir da dukan kekunan yaƙinsa. Sojojin Edom suka kewaye shi a can, amma da dare sai Yoram ya ɓarke ya gudu, sojojinsa kuma suka watse zuwa gidajensu. 22Har yă zuwa yau, Edom tana yi wa Yahuda tawaye. A lokaci ɗaya ne Libna ma ta yi tawaye. 23Game da waɗansu abubuwan da suka faru a zamanin Yoram, ba suna a rubuce a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba? 24Yoram ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda. Sai Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Copyright information for
HauSRK