Acts 22:6-16
6“Wajen tsakar rana da na yi kusa da Damaskus, ba zato ba tsammani sai wani babban haske daga sama ya haskaka kewaye da ni. 7Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, ‘Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?’ 8“Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ya amsa ya ce, ‘Ni ne Yesu Banazare, wanda kake tsanantawa.’ 9Abokan tafiyata suka ga hasken, amma ba su fahimci muryar mai magana da ni ba. 10“Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’ 11Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni. 12“Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai. 13Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa. 14“Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa. 15Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji. 16Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’
Copyright information for
HauSRK