Exodus 20:1-17
Dokoki goma
(Maimaitawar Shari’a 5.1-21)
1Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce, 2“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.3“Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.
4Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. 5Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, 6amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.
7Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.
8Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki. 9Kwana shida za ka yi dukan aikinka, 10amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai. 11Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
12Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
13Ba za ka yi kisankai ba.
14Ba za ka yi zina ba.
15Ba za ka yi sata ba.
16Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.
17Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”
Copyright information for
HauSRK