Exodus 25:1-9
Hadayu don tabanakul
(Fitowa 35.4-9)
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar. 3“Ga iri jerin kayan da za ka karɓo daga hannunsu,“zinariya, da azurfa, tagulla,
4shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin,
da gashin akuya,
5fatun ragunan da aka wanke, fatun awaki masu kyau,
itacen akashiya,
6mai domin fitila,
kayan yaji domin man keɓewa da kuma turare mai ƙanshi,
7da duwatsun Onis, da duwatsun da za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
8“Sa’an nan ka sa su yi mini wuri mai tsarki, domin in zauna a cikinsu. 9Ka ƙera wannan tabanakul da duk kayan da suke ciki da waje, daidai yadda zan nuna maka.
Copyright information for
HauSRK