‏ Exodus 25:10-22

Akwatin alkawari

(Fitowa 37.1-9)

10“Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 11Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya. 12Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe. 13Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. 14Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa. 15Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba. 16Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.

17“Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 18Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin. 19Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya. 20Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. 21Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki. 22Can, a bisa murfin da yake tsakanin kerubobi biyu da suke bisa akwatin alkawari na Shaida, zan sadu da kai, in kuma ba ka dukan umarnai domin Isra’ilawa.
Copyright information for HauSRK