Exodus 25:23-30
Tebur
(Fitowa 37.10-16)
23“Ka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 24Ka dalaye shi da zinariya zalla ka kuma yi masa ado kewaye da gurun zinariya. 25Ka yi dajiya mai fāɗin tafin hannu, ka kuma yi wa dajiyar ado da gurun zinariya. 26Ka yi zoban zinariya huɗu domin teburin, ka daure su a kusurwoyi huɗu, inda ƙafafu huɗun suke. 27Zoban za su kasance kusa da dajiyar don riƙe sandunan da za a yi amfani don ɗaukar teburin. 28Ka yi sandunan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya, da sandunan ne za ku riƙa ɗaukan teburin. 29Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu. 30Ka sa burodin Kasancewa a kan wannan tebur, yă kasance a gabana kullum.
Copyright information for
HauSRK