‏ Exodus 25:31-40

Wurin ajiye fitila

(Fitowa 37.17-24)

31“Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi. 32Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen. 33Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan. 34A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni. 35Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka. 36Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.

37“Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta. 38Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya. 39Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka. 40Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.
Copyright information for HauSRK