‏ Exodus 26:15-30

(Fitowa 36.20-34)

15“Ka yi tabanakul da katakon itacen ƙiryar da aka kakkafa a tsaye. 16Tsawon kowane katako zai zama kamu goma, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi, 17ka kafa katakan suna duban juna. Ka yi da dukan katakan tabanakul haka. 18Ka shirya katakai ashirin a gefen kudu na tabanakul, 19ka kuma yi rammuka arba’in da azurfar da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin rammukan. 20Game da ɗayan gefen, gefen arewa na tabanakul, za ka kafa katakai ashirin, 21da rammukan azurfa arba’in, biyu a ƙarƙashin kowane katako. 22Ka kafa katakai shida don can ƙarshen katakan, wato, a wajen yamma na ƙarshen tabanakul, 23ka kuma kafa katakai biyu a kusurwoyi can ƙarshe. 24Za a haɗa katakan nan a kusurwa daga ƙasa zuwa sama a daure su. Haka za a yi da katakan kusurwa na biyu. 25Ta haka za a sami katakai takwas da rammukansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da rammuka biyu.

26“Ka kuma yi sanduna da itacen ƙirya. Sanduna biyar domin katakai na gefe ɗaya na tabanakul, 27biyar domin katakai wancan gefe, biyar kuma domin na gefe wajen yamma, can ƙarshen tabanakul. 28Sandan da yake tsakiyar katakan, zai bi daga wannan gefe zuwa ƙarshen wancan gefe. 29Ka dalaye dukan katakan da zinariya, ka kuma yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Ka kuma dalaye sandunan da zinariya.

30“Ka yi tabanakul bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.
Copyright information for HauSRK