Exodus 28:1-14
Rigunan firistoci
(Fitowa 39.1-7)
1“Ka sa a kawo maka Haruna ɗan’uwanka, tare da’ya’yansa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar daga cikin Isra’ilawa, domin su yi mini hidima a matsayin firistoci. 2Ka yi tufafi masu tsarki domin ɗan’uwanka Haruna, domin a girmama, a kuma ɗaukaka shi. 3Ka faɗa wa dukan gwanayen da na ba su hikima a irin abubuwan nan, cewa su yi tufafi saboda Haruna, don a tsarkakewarsa, domin yă yi mini hidima a matsayin firist. 4Waɗannan su ne tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da efod, da taguwa, da doguwar riga, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna da’ya’yansa, waɗannan tsarkaka tufafi, don su zama firistoci masu yi mini hidima. 5Ka sa su yi amfani da zinariya, da zare mai ruwan shuɗi da shunayya da ja, da kuma lallausan lilin.Efod
(Fitowa 39.2-7)
6“Ka yi efod da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da kuma lallausan lilin, aikin gwani mai sana’a. 7Za a yi fele biyu, gaba da baya, sa’an nan a haɗa, a ɗinka a mahaɗinsu a kafaɗa. 8Za a yi mata abin ɗamara da irin kayan da aka yi efod da shi, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin. 9“Ka ɗauki duwatsu biyu masu daraja, ka rubuta sunayen’ya’yan Isra’ila a kai 10bisa ga haihuwarsu, sunaye shida a kan dutse ɗaya, saura shida kuma a kan ɗaya dutsen. 11A rubuta sunayen’ya’yan Isra’ila a kan duwatsu biyun, yadda mai yin aiki da dutse mai daraja yakan zāna hatimi. Sa’an nan a sa kowane dutse a cikin tsaiko na zinariya 12a ɗaura su a kan ƙyallen kafaɗa efod a matsayin duwatsun tuni ga’ya’yan Isra’ila. Haruna ne zai ɗauki sunayen a kafaɗarsa don tuni a gaban Ubangiji. 13Ka yi tsaiko na zinariya 14da tuƙaƙƙun sarƙoƙi biyu kamar igiya, na zinariya zalla, ka kuma ɗaura wa tsaikunan nan biyu tuƙaƙƙun sarƙoƙi.
Copyright information for
HauSRK