‏ Exodus 28:31-43

Sauran rigunan firistoci

(Fitowa 39.22-26,30,31)

31“Ka yi taguwar efod da shuɗi duka, 32ka yanke wuya a tsakiyarta don sawa. A kuma naɗe wuyan rigar yă yi kauri domin kada yă yage. 33Za a yi wa bakin rigar ado da fasalin’ya’yan rumman masu launin shuɗi, da shunayya, da mulufi. A sa ƙararrawa ta zinariya a tsakankaninsu. 34Za ka jera su bi da bi, wato,’ya’yan rumman na biye da ƙararrawar zinariya kewaye da bakin rigar. 35Dole Haruna yă sa shi sa’ad da yake hidima. Za a ji ƙarar ƙararrawar sa’ad da zai shiga Wuri Mai Tsarki a gaban Ubangiji, da sa’ad da ya fita, don kada yă mutu.

36“Ka yi allo na zinariya zalla, ka kuma yi rubutu a kansa kamar na hatimi, haka, Mai tsarki ga Ubangiji.

37Ka ɗaura shi da igiyar ruwa bula domin a haɗa shi da rawani; zai kasance a gaban rawanin. 38Zai kasance a goshin Haruna, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa baye-bayensu masu tsarki. Zai kasance a goshin Haruna kullayaumin, domin su zama abin karɓa ga Ubangiji.

39“Ka saƙa doguwar riga da lallausan lilin ka kuma yi hula da lallausan zaren lilin, ka kuma saƙa abin ɗamara mai ado.

(Fitowa 39.27-29)

40“Ka saƙa doguwar riga, abin ɗamara da kuma huluna domin’ya’yan Haruna, don yă ba su girma da ɗaukaka. 41Bayan ka sa waɗannan riguna wa ɗan’uwanka Haruna da’ya’yansa, ka shafe su da mai, ka kuma naɗa su. Ka keɓe su domin su yi mini hidima a matsayin firistoci.

42“Ka yi’yan wandunan ciki na lilin don su rufe tsiraicinsu, tsayinsu zai kama daga kwankwaso zuwa cinya. 43Dole Haruna da’ya’yansa su sa su sa’ad da za su shiga Tentin Sujada, ko sa’ad da suka kusace bagade domin hidima a Wuri Mai Tsarki, don kada su yi laifi, su kuma mutu.

“Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa Haruna da zuriyarsa har abada.
Copyright information for HauSRK