‏ Exodus 30:1-5

Bagaden turare

(Fitowa 37.25-28)

1“Ka yi bagade da itacen ƙirya don ƙona turare. 2Zai zama murabba’i, tsawon zai zama kamu ɗaya, fāɗi kuma kamu ɗaya, amma tsayin yă zama kamu biyu, ƙahoninsa kuma su zama ɗaya da shi. 3Ka dalaye bisansa da kuma dukan gefe-gefensa da kuma ƙahoninsa da zinariya zalla, ka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi. 4Ka yi zobai biyu na zinariya domin bagade a ƙarƙashin zubin, biyu a gefe da gefe su fuskanci juna, don su riƙe sandunan da ake amfani da su don ɗaukarsa. 5Ka yi sandunan nan da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya.
Copyright information for HauSRK