‏ Exodus 30:18-21

18“Ka yi daro na tagulla, ka yi masa ƙafafun da za a ajiye shi da tagulla don wanki. Ka ajiye shi tsakanin Tentin Sujada da bagade, ka zuba ruwa a ciki. 19Haruna da’ya’yansa maza za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu da ruwan da yake cikinsa. 20Duk lokacin da suka shiga Tentin Sujada, za su yi wanka, don kada su mutu. Duk lokacin da suka yi kusa da bagade don hidima ta miƙa hadayar da aka yi wa Ubangiji da wuta, 21za su wanke hannuwansu da ƙafafunsu, don kada su mutu. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla domin Haruna da zuriyarsa daga tsara zuwa tsara.”
Copyright information for HauSRK