‏ Exodus 30:22-38

Man shafewa

(Fitowa 37.29)

22Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, 23“Ka ɗauki waɗannan kayan yaji masu kyau, shekel 500 na ruwan mur, rabin turaren sinnamon mai daɗin ƙanshi shekel 250, shekel 250 na turaren wuta mai ƙanshi, 24shekel 500 na kashiya, duk bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, da moɗa na man zaitun. 25Da waɗannan za ka yi man shafewa mai tsarki, yadda mai yin turare yake yi. Zai zama man shafewa mai tsarki. 26Sa’an nan ka yi amfani da shi don shafa wa Tentin Sujada, da akwatin alkawari, 27da tebur da kuma dukan kayansa, da wurin ajiye fitila da dukan kayansa, da bagaden ƙona turare, 28bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, da daro da mazauninsa. 29Za ka tsarkake su don su zama mafi tsarki, kuma duk abin da ya taɓa su, zai zama mai tsarki.

30“Ka shafe Haruna da’ya’yansa maza, ka kuma tsarkake su don su yi mini hidima a matsayin firistoci. 31Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Wannan mai, zai zama mai tsarki ne a gare ni don shafewa, daga tsara zuwa tsara. 32Kada a zuba a jikunan mutane, kada kuma a yi wani mai irinsa. Wannan mai, mai tsarki ne, za ku kuma ɗauke shi a matsayi mai tsarki. 33Duk wanda ya yi irin wannan mai, duk wanda kuma ya shafa shi a kan wani wanda yake ba firist ba, za a ware shi daga mutanensa.’ ”

Turare

34Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ɗauki kayan yaji mai ƙanshi, resin na gum, da onika, da galbanum, da kuma zallan lubban, duk nauyinsu yă zama daidai. 35Ka yi turare mai ƙanshi yadda mai yin turare yake yi. A sa masa gishiri, yă zama tsabtatacce, tsarkakakke. 36Ka ɗiba kaɗan daga ciki, ka niƙa, ka ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin Tentin Sujada, inda zan sadu da kai. Zai zama mafi tsarki a gare ku. 37Kada ku yi wani turare irinsa wa kanku; ku ɗauke shi a matsayi mai tsarki ga Ubangiji. 38Duk wanda ya yi irinsa don jin daɗin ƙanshinsa, dole a ware shi daga mutanensa.”
Copyright information for HauSRK