Exodus 34:18-26
18“Sai ku yi Bikin Burodi Marar Yisti. Ku kuma ci burodi marar yisti har kwana bakwai, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a ƙayyadadden lokacinsa a watan Abib, gama a cikin watan ne kuka fita daga Masar. 19“Ɗan fari na kowane mutum zai zama nawa, har da ɗan farin na dabbobi, ko na garken shanu ko na tumaki. 20Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk’ya’yan farinku maza. “Kada wani yă zo gabana hannu wofi. 21“Kwana shida za ku yi aiki, amma a rana ta bakwai za ku huta; ko da lokacin noma ne, ko lokacin girbi, sai ku huta. 22“Ku kiyaye Bikin Makoni wato, bikin girbin nunan fari na alkama, da Bikin Gama Tattara amfanin gonaki, a ƙarshen shekara. 23Sau uku a shekara, dukan mazanku za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, Allah na Isra’ila. 24Zan kore al’umma daga gabanku, in fadada kan iyakarku, babu wanda zai yi ƙyashin ƙasarku a lokutan nan uku na shekara da kuka haura don ku bayyana a gaban Ubangiji, Allahnku. 25“Kada ku miƙa mini jinin hadaya tare da wani abin da yana da yisti, kada kuma ku bar kowace hadaya ta Bikin Ƙetarewa ta kwana. 26“Ku kawo nunan farin amfanin gonarku mafi kyau a gidan Ubangiji, Allahnku. “Kada ku dafa ɗan akuya a cikin madarar mahaifiyarsa.”
Copyright information for
HauSRK