Exodus 35:10-19
10“Duk waɗanda suke da fasaha a cikinku, su zo su yi dukan abin da Ubangiji ya umarta, 11“wato, aikin tabanakul da tentinsa tare da murfinsa, maɗauransa, katakansa, sandunansa da tussansa;12akwatin alkawari da sandunansa, murfin kafara da labulen da ya rufe shi;
13tebur da sandunansa, da dukan kayansa da kuma burodin kasancewa;
14wurin ajiye fitila da yake don fitilu da kayayyakinsa, fitilu da mai don fitila;
15bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul;
16bagaden hadaya ta ƙonawa da rigarsa ta tagulla da sandunansa da duk kayayyakinsa, daron tagulla da wurin ajiye shi.
17Labulen filin tenti da sandunansa da tussansa, da kuma labulen ƙofar shiga fili;
18turakun tenti don tabanakul da kuma don filin, da igiyoyinsu;
19saƙaƙƙun riguna na sawa don hidima cikin wuri mai tsarki da tsarkakakkun riguna na Haruna firist, da riguna don’ya’yansa maza lokacin da suke aiki a matsayin firistoci.”
Copyright information for
HauSRK