‏ Exodus 36:20-34

(Fitowa 26.15-30)

20Suka yi katakan tabanakul da itacen ƙirya. 21Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi, 22tare da katakai a fiƙe ɗaura da juna. Haka suka yi da dukan katakan tabanakul. 23Suka yi katakai ashirin don gefen kudu na tabanakul 24suka kuma yi rammukan azurfa arba’in don katakan su shiga ƙarƙashinsu, rammuka biyu domin kowane katako, ɗaya ƙarƙashin kowanne da aka fiƙe. 25A ɗaya gefen, gefen arewa na tabanakul, suka yi katakai ashirin 26da rammuka arba’in na azurfa, biyu-biyu don kowane katako. 27Suka yi katako shida don iyaka ta ƙarshe, wato, gefen yamma na tabanakul, 28aka kuma yi katakai biyu domin kusurwoyi tabanakul a iyaka ta ƙarshe. 29A waɗannan kusurwoyi biyu, an ninka katakan sau biyu daga ƙasa har sama, aka kuma sa su cikin zobe guda; dukansu biyu an yi su daidai. 30Ta haka aka sami katakai takwas da rammukan azurfa goma sha shida, biyu-biyu a ƙarƙashin kowane katako.

31Suka kuma yi sanduna na itace ƙirya, biyar domin katakan da suke a gefe guda na tabanakul, 32biyar domin waɗanda suke ɗayan gefen da kuma biyar domin katakan da suke gefen yamma na iyaka ta ƙarshen tabanakul. 33Suka sa sandan da yake a tsakiya yă wuce daga wannan gefe zuwa wancan. 34Sai suka dalaye katakan da zinariya, suka yi zoban zinariya don su riƙe sandunan. Suka kuma dalaye sandunan da zinariya.
Copyright information for HauSRK