‏ Exodus 37:1-9

Akwatin alkawari

(Fitowa 25.10-22)

1Bezalel ya yi akwatin alkawari da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kamu ɗaya da rabi. 2Ya dalaye shi da zinariya zalla, ciki da waje, ya kuma yi zubin zinariya kewaye da shi. 3Ya yi masa zubi huɗu na zoban zinariya, ya kuma ɗaura su a ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a wannan gefe da kuma biyu a wancan. 4Sa’an nan ya yi sanduna na itacen ƙirya, ya dalaye shi da zinariya. 5Sai ya sa sandunan a cikin rammukan da suke gefen Akwatin don ɗaukarsa.

6Ya yi murfin jinƙai da zinariya zalla, wato, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi. 7Sa’an nan ya yi kerubobi biyu da ƙeraren zinariya a ƙarshen murfin jinƙan. 8Ya yi kerub a iyakar gefe ɗaya, ya yi ɗayan kuma a wancan gefe; a iyakan nan biyu, ya yi su a haɗe da murfin. 9Kerubobin suka buɗe fikafikansu sama, suka inuwatar da murfin da fikafikansu. Kerubobin suna fuskantar juna, suna kuma kallon murfin.
Copyright information for HauSRK