Exodus 37:10-16
Tebur
(Fitowa 25.23-30)
10Suka yi tebur da itacen ƙirya, tsawonsa ƙafa biyu, fāɗinsa ƙafa ɗaya, tsayinsa kuma ƙafa ɗaya da rabi. 11Sa’an nan suka dalaye shi da zinariya zalla, suka kuma yi zubi na zinariya kewaye da shi. 12Suka kuma yi masa baki mai fāɗin tafi hannu, suka yi zubin zinariya a bisa bakin. 13Suka yi zubin zobai huɗu na zinariya don tebur ɗin, sai suka ɗaura su a kusurwoyi huɗu inda ƙafafu huɗun suke. 14Sa’an nan aka sa zoban kurkusa da bakin don riƙe sandunan da ake amfani da su wurin ɗaukan teburin. 15An yi sandunan da ake ɗaukan tebur da itacen ƙirya, aka kuma dalaye su da zinariya. 16Suka kuma yi duk kayayyakin teburin da zinariya zalla, farantansa, kwanonin tuya, kwanoninsa, da kuma butoci domin hadaya ta sha.
Copyright information for
HauSRK